Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta musanta jita-jitar da ta bazu a kafafen sada zumunta cewa shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, an sallame shi daga muƙaminsa.
Jita-jitar ta bazu ne a WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta, inda ake cewa Shugaba Bola Tinubu ya sauya Yakubu da Farfesa Bashiru Olamilekan.
- Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
- INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye
Sai dai, Kakakin Shugaban INEC, Mr. Rotimi Oyekanmi, ya bayyana cewa wannan labari ba gaskiya ba ne, kuma ya bukaci jama’a su yi watsi da shi. Ya ƙara da cewa,
“Don Allah, ku yi watsi da wannan labari. Ba gaskiya ba ne.”
Farfesa Yakubu yana cikin wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe a matsayin Shugaban INEC, wanda zai ƙare daga nan gaba a wannan shekarar 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp