Ya dawo gida daga Amurka ba, amma ba a matsayin wanda ya yi ritaya ba, illa kawai don sake fasalin jihar baki-ɗaya, musamman ta fuskar inganta masana’antu.
Daga Gudi Zuwa Ɗaukaka
A ƙauyen Gudi, inda suke da al’adu daban-daban tare da zaman lafiya, a nan Abdullahi Sule ya fara koyon horon aiki.
An haife shi a ranar 26 ga Disambar 1959, barin garinsu da ke Nasarawa zuwa yunƙurin kawo sauyi a jihar, na da alaƙa da kyakkyawar manufa da kuma hangen nesa.
- Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa
- ‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
Sai ga shi yau, yaron da fito daga Gudi ya kasance a matsayin mai tsara yadda za a inganta masana’antu a Jihar Nasarawa, kuma shugaba gogagge, wanda ya zagaya duniya tare da sanin matsalolin gida, wannan ne yasa labarinsa ya yi fice a Arewacin Nijeriya.
Injiniya Mai Matuƙar Hangen Nesa
Tun kafin ya shiga siyasa, Sule ya kasance mutum mai gaskiya da aiki tuƙuru. Bayan kammala karatun digirinsa na farko da na biyu a Amurka, duk a fannin Injiniyarin da Fasahar Masana’antu, B.Sc da M.Sc daga Jami’ar Jihar Indiana, ya kuma haɓaka ƙwarewarsa a manyan kamfanonin injiniya na Amurka, daga Dril-Ƙuip zuwa Kamfanin Osyka, inda ya zama daraktan ci gaban kasuwanci na Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Lokacin da ya dawo Nijeriya, a shekara ta 2000, ba kawai da takaddun shaida ya dawo ba, ya dawo ne da cikakkiyar ƙwarewa. Shi ne ya kafa kamfanin mai na Sadiƙ Petroleum, ya jagoranci tafiyar da kamfanin na ‘African Petroleum Plc’, sannan ya zama Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Siga na Dangote, inda ya yi ƙaurin suna wajen inganci da ƙirƙire-ƙirƙire.
Waɗannan abubuwa, sun ne suka zama ginshiƙan manufar siyasarsa, wajen tafiyar da Jihar Nasarawa; musamman ta fuskar kasuwanci.
Hange Da Dabarunsa Na Aiki
Lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna, Gwamna Sule ya zo da wani shiri, mai suna ‘Nassarawa Economic Deɓelopment Strategy (NEDS)’.
Wannan ita ce cikakkiyar taswirar ci gaban jihar ta farko, wadda aka gina ta a kan masana’antu da samar da ababen more rayuwa, ci gaban kasuwancin al’umma da kuma shugabanci na gari.
NEDS, ta sake fasalin yanayin tattalin arziƙin Jihar Nasarawa, daga yankin noma zuwa wani yanki na saka hannun jari.
A ƙarƙashin jagorancinsa, jihar ta jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje a masana’antu, ma’adanai, wutar lantarki da noma, inda ya mayar da Jihar Nasarawa matsayin cibiyar masana’antu ta Nijeriya.
Hasashensa na tattalin arziƙi, na da inganci kamar yadda yake da buri: mayar da fa’idar da jihar ke da ita cikin ma’adanai masu ƙarfi, kusanci da Abuja da yawan sanya matasa yin gasa a tsakaninsu.
Masana’antu A Matsayin Ginshiƙin Ci Gaba
Tsarin mulki na Gwamna Sule, yana ɗaukar masana’antu a matsayin abubuwan more rayuwa. Tun daga fafutukar ci gaban birane da gwamnatinsa ta yi na gina manyan titunan birane zuwa wuraren shaƙatawa na masana’antu a ƙauyen Nasarawa, zuwa ayyukan makamashin da za a sabunta, jihar na ci gaba da zama babbar wata hanya ta zuba jari.
Ta hanyar haɗin gwiwa da gangan, Jihar Nasarawa ta jawo hankalin kamfanoni, domin samar da siminti, ma’adanan lithium, sarrafa ethanol, samar da ayyukan yi, kuɗaɗen shiga da sauransu.
Haɗin gwiwar da jihar ke yi da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), kan amfani da iskar gas da kafa aikin haƙo mai da iskar Gas na Nasarawa, ya nuna ƙwaƙƙwaran matakai na samun wadatar makamashi da matuƙar ƙima.
Ayyukan Ababen More Rayuwa Da Sha’anin Mulkin
Yunƙurin sabunta ababen more rayuwa na Gwamna Sule, abu ne da ya samo asali. Hanyoyi, Makarantu da asibitoci, sun bazu a ko’ina cikin ƙananan hukumomi, don tabbatar da ganin cewa; ba a bar al’umma a baya ba.
Bayan ayyuka na zahiri, ana ayyana mulkinsa ta hanyar bayyana gaskiya, haɗin gwiwar jama’a da sake fasalin hukumomi.
Gwamnatinsa ta ɓullo da tsarin gudanar da filaye a zamanance, gyare-gyaren haraji wanda ya dace da zuba jari da tsarin PPP, wanda ke taimakawa wajen sauƙaƙa kasuwanci da samun bunƙasarsa.
Yana kuma faɗaɗa bayar da damar ilimi da sana’o’i, domin gina tushen jarin Ɗan’adam, wanda zai ci gaba da ingiza ci gaban masana’antun jihar.
Masanin Makamar Aiki A Mulki
Waɗanda suka san shi, sun bayyana Injiniya Sule ba a matsayin ɗan siyasa ba, illa a matsayin masanin makamar aiki, gogagge, mai kuma tarin ƙwarewa. Ya kawo wa gwamnatin tasa sahihancin injiniya da kuma hazaƙar da ya samu a matsayin manaja.
Tarihinsa- daga Kamfanin ‘Jos Steel Rolling Company’ zuwa na ‘African Petroleum’, sun ba shi ƙwarewar jagoranci da kuma tawali’u, musamman wajen saurarar mutane dangane matsalolinsu.














