Ƙasar Iran ta zargi Birtaniya, Faransa, da Jamus da karya alƙawuran da suka ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar JCPOA da aka cimma a shekarar 2015, bayan ƙasashen uku sun yi barazanar dawo da takunkumi karya tattalin arziƙi ga ƙasar.
An ƙulla yarjejeniyar ne domin taƙaita shirye-shiryen nukiliyar Iran a maimakon sassauta mata takunkumi, sai dai yarjejeniyar ta fara rushewa ne bayan Amurka ta fice daga ciki a 2018 a lokacin shugaba Trump, inda ta dawo da manyan takunkumin karya tattalin arziƙi kan Iran.
- Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa
- Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane
Ko da yake Turawan sun yi alƙawarin bin yarjejeniyar, da ƙoƙarinsu na rage wa Iran raɗaɗin takunkumin Amurka bai haifar da ɗa mai ido ba. Manufofin kuɗi da Turai ta ƙaddamar domin taimaka wa Iran sun gaza, kamfanoni daga yammacin duniya kuma sun fice daga Iran, lamarin da ya tsananta matsin tattalin arziƙi a ƙasar. Iran na zargin ƙasashen Turai da cewa sun tsaya ne a kan magana kawai ba tare da aiki ba.
A ranar Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baqaei, ya soki Turai bisa abin da ya kira da “gazawa da sakaci” wajen aiwatar da yarjejeniyar, yana mai kiran barazanar da suke yi a yanzu da “rashin adalci” kuma “cike da son zuciya”. Wannan na zuwa ne bayan Turawan sun nuna damuwa kan matakin da Iran ta kai na inganta sinadarin uranium zuwa kashi 60% wanda hukumar IAEA ta ce ya ninka ƙima mafi girma da yarjejeniyar JCPOA ta amince da shi wato 3.67%.
Ƙasashen Birtaniya, Faransa da Jamus na shirin amfani da tsarin “snapback” na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ke ba su damar dawo da takunkumi idan aka samu Iran da laifin karya yarjejeniya. Baqaei ya kare matakin Iran da cewa ƙasar ta fara rage bin yarjejeniyar ne bayan ficewar Amurka da gazawar Turai wajen cika alƙawari, yana mai cewa duk matakan Iran sun yi daidai da sharuɗɗan yarjejeniyar dangane da martani na musaya.
Wannan rikici ya ƙara jaddada gazawar yarjejeniyar ta JCPOA kuma ya tayar da ƙarin shakku kan yiwuwar dawo da tattaunawar diflomasiyya don taƙaita shirye-shiryen nukiliyar Iran. Tunda kowanne ɓangare ke jifan ɗayan da laifi, yanzu dai alamar dawowa ga yarjejeniyar 2015 na ƙara dusashewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp