Isra’ila ta fara aiwatar da shirin sakin fursunonin Falasdinawa 369, ciki har da 36 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai, a wani mataki da ke janyo hankalin duniya.
A daren jiya ne wata motar ƙirar bas mai ɗauke da rukuni na farko na waɗanda aka sako ta isa birnin Beitunia da ke Yammacin Kogin Jordan, inda dubban ‘yan uwa da magoya baya suka tarɓe su cikin farin ciki da murna.
- Wakilin Sin Ya Yi Tir Da Harin Isra’ila Kan Cibiyoyin Kiwon Lafiya A Gaza
- Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Duk da farin ciki, alamun wahala da rashin lafiya sun bayyana a jikin wasu daga cikin fursunonin. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Crescent ta Falasɗinu ta bayyana cewa an gaggauta kai mutum huɗu daga cikinsu don duba lafiyarsu.
Sakin fursunonin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da matsin lamba kan Isra’ila domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya, yayin da duniya ke sa ido kan ci gaban lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp