Saudiya ta yi tir da hare-haren da Isra’ila ta kai kan Iran, tana mai cewa ƙaruwar wannan tashin hankali na barazana ga kwanciyar hankali a yankin.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta bayyana damuwa, tana mai nuna harin a matsayin take haƙƙin ƙasar Iran da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa.
- Biden Da Netanyahu Sun Tattauna Kan Shirin Isra’ila Na Kai Wa Iran Harin
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Masar Da Iran
“Daular Saudiyya ta bayyana tir da harin Soji da aka kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya zama take haƙƙinta da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa,” in ji ma’aikatar a shafinta na X (da aka fi sani da Twitter a baya).
Saudiyya ta yi kira ga kowane ɓangare da ya yi hattara, tana mai gargaɗin cewa yaɗuwar rikicin na iya haifar da tasirin tsaro mai muni ga ƙasashen yankin.
Hare-haren, wanda Isra’ila ta ce martani ne ga wasu hare-haren da ta danganta wa Iran, sun shafi wurare daban-daban a Iran, ciki har da wuraren Soji a Tehran da sansanonin kusa da shi.