Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya tattauna da Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ta wayar tarho.
Shugabannin biyu sun tattauna kan martanin da Isra’ila ke shirin dauka kan harin makamai masu linzamin da Iran ta kai kasar a makon da ya wuce daidai lokacin da ake fargabar kada yakin ya karade yankin Gabas ta Tsakiya.
- Dorewar Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Ta Karawa Duniya Kwarin Gwiwa
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Mara Baya Ga Kasashen Yankin Manyan Tafkunan Afirka Don Karfafa Hadin Gwiwa
Fadar White House ta ce mataimakiyar shugaban kasar, Kamala Harris ta shiga tattaunawar da aka yi a ranar Laraba.
Sai dai kawo yanzu ba a bayyana ainahin abin da shugabannin suka tattauana a kai ba.
A gefe guda, ministan tsaron Isra’ila, Yoav Gallant, ya ce martanin da za su mayar wa Iran, zai kasance na bazata.
“Ba za su taba fahimtar abin da ke faruwa ba, ko ta yaya ya faru, sai dai kawai su ga barna, shammatarsu za mu yi,” in ji shi.
Har wa yau, a Gabas ta Tsakiya, ana ci gaba da tafka yaki tsakanin sojin Isra’ila da mayakan Hezbollah.
Harin makamai masu linzamin Isra’ila ya hallaka mutum hudu a wani kauye da ke birnin Sidon na Lebanon.
A yayin da kuma harin makamin roka ya halaka Isra’ilawa biyu a Kiryat Shmona na Arewacin kasar.