Mayakan kungiyar ISWAP sun hallaka kwamandan Boko Haram mai shugabantar kungiyar a Sambisa da Gwoza, Ali Gana Alhaji Ali a dajin Gwoza da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Majiyar tsaro ta shaida wa Daily Trust cewa, Ali na daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Boko Haram, an kashe shi ne a wani farmakin da mayakan ISWAP suka kaddamar a kan ‘ya’yan kungiyar a ranar Lahadi.
- An Kashe ‘Yan Ta’adda 41 Yayin Da Boko Haram Da ISWAP Suka Bai Wa Hammata Isla A Borno
- ‘Yan Boko Haram Sun Saki Mata 48 Da Suka Yi Garkuwa Da Su A Borno
“Shi ne mataimakin marigayi Ali Ndulde, baya ga Shekau, babu wani mutum da ya kashe mutane kamarsa a dukkanin dajin Sambisa da Bayan Dutsen Gwoza.
“Shahararren makashi ne. Aikin ta’addancinsa a yankin Gwoza ya sanya al’ummar kauyuka, manoma da mazauna yankin Pulka, Bankin, Bama da Gwoza Mubi cikin tsananin fargaba da tsoro da zullumi.
“Ba su daukan fursuna balle ma su ajiyesu, suna yankan rago ga mutane a kusan kowane sati a gonakansu. Tabbas al’ummar Gwoza za su yi murna da maraba bisa jin labarin mutuwarsa,” inji majiyar.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan shekaru biyu da babban kwamandan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya tarwatsa kansa da kansa a wani mummunar gumurzu da suka yi da mayakan ISWAP a watan Mayun 2021.
A makon da ya gabata ne, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gwoza, Damboa da Chibok a majalisar wakilai ta tarayya, Usman Ahmed Jaha, ya nuna damuwarsa dangane da kisan manoma 10 a cikin kwanaki 10 a yankin Goza.
Ya yi korafin cewa ana kashe manoma kusan kullum a yankin a yayin da suke kokarin ciro amfanin gonakansu.