Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe masunta 35 ’yan gudun hijira da suka je yin su a yankin Mukdolo da ke Karamar Hukumar Ngala ta Jihar Borno.
Wani masunci da ya tsallake rijiya da baya ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Laraba ne mayakan na ISWAP sun ritsa su ne ta gabar kogi, suka bude musu wuta inda mutum 35 suka mutu, wasu da dama kuma ba a san inda suka shige ba.
- Zaben Gwamnoni: Kotu Ta Bai Wa INEC Umarnin Amfani Da Katin Zabe Na Wucin Gadi
- Taruka 2 Na Kasar Sin: A Kara Fahimtar Cikakken Tsarin Demokuradiyya Da Ake Damawa Da Jama’a
Ya ce “Sun bullo ne daga cikin kungurmin daji a kan babura, suka zagaye mu ta gabar kogin, cewa ‘mun sha jan kunnenku cewa ku daina zuwa nan, amma sai kuka rika gaya wa sojoji inda muke.
“Daga nan suka fara harbi ta kowace kusurwa, mutum uku kacal suka koma Dikwa da ransu, amma ina tabbatar da cewa mutum sama da 35 aka kashe; yanzu haka mutane da yawa ba su dawo garin Dikwa ba.”
Ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Mukdolo da ke kusa da garin Dikwa kuma daukacin ’yan gudun hijirar sun fito ne daga Dikwa.
Da yake tabbatar da labarin harin, Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tayar da kayar baya da kuma sharhi kan sha’anin tsaro a yakin Tabkin Chadi, ya ce an gano gawar mutum 26 daga cikin ’yan gudun hijirar da kungiyar ta kashe.
Ya ce mutum tara daga cikin masuntan da aka kai wa hari sun tsira, amma uku daga cikinsu sun samu raunukan harbi.
Ya bayyana cewa sai da mayakan “Suka sa mutanen kwantawa, suka daddaure su da ragar kamun kifi, sannan suka har suka galabaita, sannan suka bude musu wuta.
“Sojoji sun gano gawarwakin mutum 26 a cikin daji bayan da suka samu labarin abin da ya faru daga sauran wadanda suka tsare,” in ji shi.