Iyalan sarkin Okoloke na jihar Kogi, Oba James Dada Ogunyanda, sun yi kira ga al’umma don taimakawa wajen tara kuɗin fansa Naira miliyan ₦50 da masu garkuwa suka buƙata. An sace Sarkin ne daga fadarsa a Yagba West LGA ranar Alhamis da ta wuce.
Duk da cewa sun tara miliyan ₦25 ta hanyar sayar da kayansu, iyalan sun ce wasu ‘yan siyasa da suke tsammanin za su taimaka sun har yanzu sun ji shiru. “Wasu ma sun toshe wayoyinmu,” in ji wani ɗan gidan, yana nuna damuwarsu game da yawan rashin lafiyar Sarkin da ke hannun masu garkuwa tsawon kwana 5.
- Zargin Kin Amincewar Kwankwaso Zuwa APC: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Mai Taimaka Ma Ta
- An Cafke Mai Garkuwa Da Mutane A Sansanin Alhazan Abuja
Masu garkuwar sun fara buƙatar miliyan ₦100 kafin su rage zuwa miliyan 50. Iyalan sun ƙaryata labarin cewa an ƙara rage kuɗin zuwa miliyan, suna mai cewa har yanzu masu garkuwar sun dage kan miliyan 50.
Sun yi kira ga manyan ‘yan siyasa na Kogi ciki har da Sanata Dino Melaye, Sanata Sunday Karimi, Hon Leke Abejide, Hon Faleke da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da su taimaka wajen cikasa sauran kuɗin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp