Jiya ne, jakadan kasar Sin dake Niger Jiang Feng da shugaban kasar Mohamed Bazoum sun halarci bikin kaddamar da aikin gyara hanyar Abalak zuwa Tamaya da Sin ta ba da taimakon gyarawa. Ministoci da manyan jami’an gwamnatin kasar da wakilan bangarorin daban-daban kimanin dubu 1 ne suka halarci bikin.
A jawabinsa shugaba Mohamed Bazoum ya ce, hanyar za ta hade kudanci da arewacin kasar, matakin da zai ingiza mu’amalar albarkatu da ma karfafa bunkasuwar tattalin arzikin kasar, Niger na matukar godiya kan tallafin da Sin ta dade take baiwa kasar, yana mai fatan kara hadin kai da Sin don zurfafa huldar abota ta yau da kullum.
A nasa bangare, jakada Jiang Feng ya ce, Sin na ci gaba da aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma aikin na wannan karo zai taimakawa Niger wajen tabbatar da hanzarta hadewar manyan ababen more rayuwa a fannin zirga-zirga, ta yadda za a ingiza karuwar tattalin arziki da ci gaban al’ummar kasar.
Ana gudanar da aikin ne a lardin Abalak na yankin Tahoua, kuma kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya gudanar da aikin. (Amina Xu)