Jakadan kasar Sin a Amurka Qin Gang, ya karyata zargin cewa wai Sin na danawa kasashen nahiyar Afirka tarkon bashi. Jakadan ya kara da cewa, kamata ya yi nahiyar Afirka ta zama wurin hadin gwiwar kasa da kasa, maimakon wani fage na gwabza takara, domin cimma burikan siyasar yankunan.
Tsokacin jakada Qin Gang, ya zo ne a jajiberin taron yaukaka dangantakar Amurka da kasashen Afirka, wanda shugaba Joe Biden zai jagoranta a birnin Washington.
Yayin kwarya-kwaryar tattaunawa da kafar watsa labarai ta Semafor dake Amurka a jiya Talata, gabanin bude taron na Washington, Qin ya ce “Ko kadan jarin da Sin ke zubawa a Afirka, da ma tallafin kudade da kasar ke baiwa nahiyar ba tarkon bashi ba ne”.
Jakadan na Sin ya yi fashin baki, game da sakamakon wani bincike da cibiyar “Debt Justice” dake Birtaniya ta wallafa a watan Yuli, inda ya ce adadin bashin da hukumomin kudi masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya ke bin kasashen Afirka, ya ninka wanda Sin ke bin kasashen nahiyar har sau 3, kuma yawan kudin ruwa da hukumomin kudin na yammacin duniya ke cazar kasashen Afirka ya ninka na kasar Sin.
Bugu da kari, jakada Qin ya tabo batun dage wa’adin biyan bashi da kasashen G20 suka gabatar, inda ya ce Sin na kan gaba wajen aiwatar da wannan manufa, inda ta zamo ta farko wajen dage wa’adin biyan bashin da take bin kasashe daban daban, cikin daukacin kasashe mambobin kungiyar ta G20.
Game da taron na Amurka da kasashen Afirka, jakadan ya ce yana fatan Amurka za ta fito da kwararan matakai da za su ingiza ci gaba da wadatar nahiyar Afirka. Kaza lika ya yi kira ga Amurka da ta yi hadin gwiwa da Sin, ta yadda a matsayin su na kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kuma mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, za su iya hada karfi da karfe wajen bunkasa zaman lafiya, da tsaro da bunkasar nahiyar Afirka.
Har ila yau, ya kamata su sauke nauyin dake wuyansu, kasancewarsu manyan kasashe da ya dace su cika alkawuran da suka dauka a matakin kasa da kasa.
Taron birnin Washington na bunkasa hadin gwiwar Amurka da kasashen Afirka, zai gudana ne tsakanin ranakun Talata zuwa Alhamis, ya kuma hallara shugabanni daga kasashen Afirka 49, da kuma sassa daban daban na masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da cinikayya. (Saminu Alhassan)