A ‘yan kwanakin nan wasu maganganu na ta yawo da karakaina musanman a shafukan sada zumunta a kan batun da ya shafi Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Abdullahi Bayero da Masarautar Kanon da ke Arewacin Nijeriya.
LEADERSHIP HAUSA ta bi kadin wannan batun don jin ra’ayoyin jama’a game da Sarkin Kano da cece-kucan da ake kan bukatar da kungiya da ake kira da ‘yan dangwale suka gabatarwa zauren majalisar dokokin Jihar Kano, kan ta rushe sababbin masarautun Kano 4 da batun sake dawo da Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi. Kan haka mun bibiyi ra’ayoyin wasu Kanawa kan batun.
- Kungiyar ‘Yan Dangwale Ta Nemi Majalisa Ta Tsige Sarakunan Kano 5 Da Dawo Da Sanusi
- Za Mu Cigaba Da Fadakarwa Kan Dorewar Zaman Lafiya Tsakanin Arewa Da Kudu – Sarkin Kano
Wani mai bibiyar al’amuran da suka shafi masarautar Kano da ya bukaci mu boye sunansa, ya bayyana mana cewa, mutanen Kano ba za su taba kaunar a raba su da Sarkin su ba, don suna kaunarsa saboda kaunarsa da son zaman lafiya ga duk Jama’ar Kano da mutanen da ke Fadar Kano, ya ce, misali na farko da zamu iya kallo don gane karamcin Sarkin Kanon tun gabanin ya zama Sarki, yana cewa, ” Mai martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero, yana cikin mutane na farko da suka yi wa, Muhammad Sunusi II, mubaya’a da ba shi gudunmowar da babu wanda ya ba shi tun daga sanda ya zama Sarki har zuwa lokacin da aka fadada Masarautun Kano zuwa gida biyar, ”
“A lokacin da aka nada Sarki Muhammad Sunusi II, al’umma sun yi bore na rashin aminta da nadin da aka yi masa, wanda har ta kai aka kwashe kwanaki 3 ana ta gudanar da zanga-zanga da kona tayoyi a birnin Kano, komai ya tsaya cak aka hana shiga gidan Dabo, a karshe gwmanatin wancan lokacin sai da ta yi amfani da ‘yan tauri wajen rako sarkin don shiga gidan Dabo.” Cewarsa.
Ya ci gaba da bayyana cewa; “ A lokacin da Sanusi ya shiga gidan Dabo, wasu daga cikin hakimai da yawa suka ki zuwa yin mubayi’a sai da shi Sarkin na yanzu Alh. Aminu Ado Bayero, ya bi su daya bayan daya yana musu nasiha kan su zo su yi wa l, Sanusi Lamido, mubaya’a tunda Allah ya ba shi, hatta ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, Sarkin Kano Aminu ne ya hada kan su don su mara wa Sarki Sunusi baya ya ci gaba da gudanar da sha’anin mulkinsa cikin natsuwa.” Cewarsa.
A bangare guda wasu masoya Sarkin na Kano, Alh. Aminu Ado Bayero, na ganin cewa tun asali ma shi ne ya nuna wa Sarki Sanusi hanyoyin da zai bi don samun soyayya daga al’ummar Kano, suka ce ta haka ne ma ya samu gagarumar nasara wajen samun soyayya jama’ar Kano a wancan lokacin.
Bangaren Muhammadu Sanusi ll
A bangare guda, su kuwa masu fata da burin dawowar Sarkin Kanon na 14, Malam Muhammadu Sanusi ll, kan karagar masarautar ta Kanon, dalilan su na dawowar tsohon Sarkin Kanon na 14 bai wuce cewa wai an cire Sarkin a wancan lokacin ba bisa ka’ida ba, kuma ba’a bi tanadin doka yayin tube rawanin Sarki Sanusi ll ba.
Wasu na ganin a dawo da Sanusi ll don ya zama an hade masaratun wuri guda da sarki daya rak.
Mai Mazauna Kano ke cewa kan batun?
Wasu mazauna Kanon na cewa indai laifi ne ke saka wa a cire Sarki to babu wanda zai iya fadar ga laifin da Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero, ya yi harda za ta kai ga cire shi, kuma duk masu yada maganar a cire shi ba su da wani dalili na laifi ko hujja kan haka, face dai su fake da cewa saboda kawai tsohon Gwamnan Kano Ganduje ne ya nada shi.
Wasu kuwa cewa suke fatan su bai wuce zaman lafiyar Kano ya dore ba, don haka a bar wannan batun na tube rawanin Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado, don gudun kar a hautsina zaman lafiyar Kano, a mayar da hankali wajen yaki da fatara da yunwa da ta addabi jama’a a yanzu.
Mai Gwmanatin Kano ta ce kan batun?
Har kawo wannan lokacin da muke hada wannan rahoton babu wata magana da ta fito daga bakin gwamnatin jihar kan batun a hukumance. Sai dai ana hango wasu makusanta gwamnatin na aike wa da shagube kan batun masarautun Kanon da ke tayar da kura a yanzu haka a Kano da kafafan sada zumunta na yanar gizo.