A yau Litinin ake sa ran cigaba da shari’ar dan majalisa tarayya, Alhassan Doguwa kan zargin kisan gilla ta hanyar kone wasu mutane har lahira a hedikwatar ofishin yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke karamar hukumar Tudun wada.
Kotun wacce ke zamanta a titin kotu Road acikin birnin Kano da farko ta tura dan majalisar gidan yari ajiya kafin a cigaba da sauraron karar a yau ranar Litinin.
Dimbin Jama’a dauke da alluna da kwalaye sun yi rubuce-rubuce ajiki, sun nemi kotun da ta yi adalci kan mutanen da aka kone kurmus har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama fitaccen dan majalisar ne mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta jihar Kano, bayan an zarge shi da jagorantar ‘yan daba, wadanda suka kai hari tare da kona ofishin jam’iyyar NNPP da ke karamar hukumar Tudun Wada, Kano, inda kuma aka kona mutane biyu kurmus a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ake tattara sakamakon zaben da aka kammala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp