Hukumar kula da shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta kaddamar da wani bita cikin gaggawa kan tsarin Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (UTME) na shekarar 2025, biyo bayan korafe-korafe da dalibai da iyaye ke yi a fadin kasar na tare da zargin rashin bin ka’ida da kuma sabani a sakamakon jarabawar.
Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan da hukumar ta sake sakamakon jarabawar bana, inda hukumar ta tabbatar da cewa ta samu jerin korafe-korafe da daman gaske. Dubban dalibai ne dai suka yi fatali da kin amincewa da sakamakon da suka samu a jarabawar, lamarin da ke janyo kokonto da shakku kan ingancin tsarin da ake bi.
- JAMB Ta Dakatar Da Wasu Jami’anta Saboda Tilastawa Wata Daliba Cire Hijabi
- Gwamnatin Kano Ta Soke Tsaftar Muhalli A Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB
Dalibai da dama sun shiga shafukan sada zumunta, suna zargin hukumar JAMB da gazawa ta bangaren samun tangardar na’ura da suka yi imanin cewa ya yi illa ga kwazonsu da kokarinsu a yayin jarabawar.
Da yake magana a Abuja, mai magana da yawun hukumar JAMB, Dakta Fabian Benjamin ya tabbatar da cewa hukumar tana duba na’urorinta a kai a kai gabanin ma gudanar da jarabawar.
“Muna hanzarta sake duba jarabawarmu na yau da kullun, wanda zai bincika kowane bangare na tsarin UTME, tun daga rajista zuwa jarrabawa da fitar da sakamako,” in ji Benjamin.
Ya yi nuni da cewa hukumar tana aiki ne tare da hadin gwiwar abokan huldar waje, da suka hada da kungiyar kwararrun na’urar kwamfuta ta Nijeriya, da manyan masu jarrabawa daga manyan makarantu, da kungiyar ilimi da cibiyar bincike a Afirka. Wadannan hadin gwiwar, in ji shi, suna da nufin samar da ingantaccen bincike da kuma sahihin bincike.
“Idan an gano cewa an samu tangarda a na’ura, to za a dauki matakan gyarawa ba tare da bata wani lokaci ba,” Benjamin ya tabbatar.
Duk da wannan tabbacin da aka bayar, sama da dalibai 8,000 ne suka shigar da korafinsu a hukumance suna cewa an samu matsaloli na na’ura sosai a yayin jarabawa. Abubuwan da aka ruwaito sun hada da daskararrun allon kwamfuta, jinkirin shiga cikin tsarin zana jarabawar daga ita kwanfutar, da karewar zaman jarrabawa ba zato ba tsammani.
Binciken farko na sakamakon UTME na 2025 ya nuna cewa sama da kashi 78 na sama da dalibai miliyan 1.9 sun samu maki kasa da 200 cikin matsakaicin maki 400. Alkaluman sun kara zurfafa shakku na gazawar fasaha ko na tsari.
Benjamin ya ce duk da haka, lamarin ya tsaya kan sakamakon kamar yadda aka fitar a halin yanzu, yana mai bayyana cewa sun yi daidai da hakikanin kwazon da dalibai suka nuna. Har ila yau, ya amince da alhakin hukumar ta binciki duk rahotannin da suka dace na abubuwan da suka faru.
Sai dai hukumar ta nemi a kwantar da hankali har zuwa lokacin da za ta kammala binciko shin an samu matsala a tsarin jarabawar ko kuma gazawar kwazon ɗalibai ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp