Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta dakatar da wasu jami’anta saboda tilastawa wata mai zana jarrabawa cire hijabi a yayin gudanar da jarrabawar a ranar Asabar din da ta gabata.
Jami’an, a daya daga cikin cibiyoyin jarrabawar da ke Legas, sun nace, cewa, cire hijabi na daya daga cikin sharuddan shiga dakin jarabawar.
- An Yi Garkuwa Da Dalibai 1,680 Da Kashe 180 Cikin Shekara 10 A Nijeriya – UNICEF
- Shawarar Tabbatar Da Tsaron Duniya: Sin Ta Zo Da Mafita Ga Alkaba’in Tashe-tashen Hankula
“Hukumar JAMB ta yi matukar bakin ciki da faruwar lamarin kuma, a kan bincike, ta gano cewa, wannan sharadi, ba shi da alaka da kowace ka’idojin jarrabawar ta Hukumar.
“Tunda rashin sanin doka ba uzuri bane, an dakatar da jami’an domin hakan ya zama izina ga wasu” in ji mai magana kan harkokin yada labarai na hukumar, Dr. Fabian Benjamin, a Abuja ranar Lahadi.