Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta janye sakamakon wata mai suna, Mmesoma Ejikeme, ‘Yar takarar Jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) kan zargin yin magudin sakamakon jarabawa na bogi.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
- Dalibai 947,000 Ne Za Su Rubuta Jarabawar JAMB Cikin Kwanaki 2
- Da Dumi-dumi: JAMB Za Ta Fara Fitar Da Sakamakon Jarrabawar UTME A Gobe Talata
Idan zaku tuna cewa Ejikeme, wadda ta yi ikirarin ta samu maki 362 a Jarabawar UTME ta shekarar 2023, inda ta samu kyautar Naira miliyan 3 daga hannun Innocent Chukwuma, shugaban kamfanin kera motoci na Innoson.
Benjamin ya ce wasu daga cikin ’yan takarar UTME na 2023 suna nuna makin bogi domin su samu damar da ba ta dace da su ba.
” Asalin sakamakonta dalibar 249 babu wanda ta yi ikirari ba saboda babu abin da zai canza sakamakon, ” Cewar Hukumar.
Don haka Hukumar JAMB zata gurfanar da dalibar a Kotu kan da’awar maki fiye da yadda suka samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp