Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce an kashe jami’ai uku da sojoji 22 a wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai a jihar Neja.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a wani sabon rahoton da rundunar sojin Nijeriya ta fitar na mako biyu.
- An Sake Gurfanar Da Emefiele A Kotu Kan Tuhume-Tuhume 20
- Yadda Sinawa Ke Kokarin Sayen Hidimomi Na Haifar Da Alfanu Ga Manyan Kamfanonin Kasa Da Kasa
Ya ce babu wata kungiya da za ta taba kai wa sojoji hari ba tare da wani mummunan sakamako ba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jirgin NAF MI-171 mai saukar ungulu ya yi hatsari a ranar 14 ga watan Agustan 2023 da misalin karfe 1 na rana kusa da kauyen Chukuba a jihar Neja.
Jirgin dai ya taso ne daga makarantar Firamare ta Zungeru zuwa Kaduna kafin faruwar mumunar lamarin.
Janar Buba ya kara da cewa jirgin na aiki kwashe sojojin da suka ji rauni kafin ya yi hatsari inda a baya sojoji 14 suka rasa rayukansu sannan bakwai kuma suka jikkata.
Ya ce jirgin yana da matukan jirgi biyu da ma’aikatansa biyu.
Cikakken bayani na tafe…