• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an DSS Sun Cafke Wani Babban Kwamandan ISWAP A Kano

by Muhammad
3 years ago
Jami'an

Rundunar tsaron farin kaya ta DSS a Nijeriya ta tabbatar da cafke wani da take zargin ɗaya ne daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ‘Yan ta’adda ta ISWAP ne a Kano.

BBC ta rawaito cewa, Rundunar tsaron ta dai kama wanda ake zargin tare da wasu daga cikin yaransa a daidai lokacin da suke shirya kai wasu hare-hare na ta’addanci a Kano.

  • Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
  • An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Mutumin, wanda jami’an DSS suka kama da ake yi wa laƙabi da Malam Abba, an kama shi ne a unguwar Samegu a yankin karamar hukumar Kumbotso a Kano.

DSS ta ce ta sami nasarar kama Malam Abba da waɗanda aka kama shi da su bayan samun wasu bayanan sirri.

Sannan wanda ake zargin shi ne mai bayar da horo, da shirya hare-haren da ISWAP din za ta kai a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban hafsan tsaro Nijeriya janar Lucky Irabor ke cewa rudunar tsaron kasar ta daƙile wani yunƙurin kai hari a Kano wanda suka ce zai iya zama “mafi muni” a ƙasar.

Janar Irabor ya ƙara da cewar sun daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari wata coci da ke garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka kashe fiye da mutum 40.

Sannan sun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su, tare da ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasar ciki har da Abuja.

Idan za a iya tunawa a ranar 17 ga watan Mayu aka sami fashewar wata tukunyar gas a titin Aba da ke Sabon gari a Kano, da ya yi sanadiyar mutuwar mutum tara tare da jikkata wasu da dama.

Sai dai an sami rabuwar kai tsakanin al’umma mazauna yankin da jami’an tsaro, inda mazauna yankin ke cewa bom ne, yayin da jami’an tsaro ke cewar tukunyar gas ce da ke waje ta fashe.

Haka zalika kwanaki kadan da faruwar wannan al’amari rudunar ƴan sandan Kano ta ce ta ga wata mota maƙare da kayan hada bom a unguwar Bugaje a yankin karamar hukumar Kumbotso.

Jami’an tsaron sun yi zargin cewar an shiga da motar ne daga jihar Jigawa da ke maƙwabtaka da Kanon.

Tuni dai hukumomi a Nijeirya suka tabbatar da ayyukan Mayakan ISWAP a jihar Kaduna da wasu dazuzzuka da ke arewa maso yammacin Nijeirya, da ake fama da matsalolin masu garkuwa da mutane.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
Manyan Labarai

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Next Post
Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Ansaru Ta Ce Ba Ita Ta Kai Hari Kan Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ba

Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Ansaru Ta Ce Ba Ita Ta Kai Hari Kan Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ba

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.