Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta ce jami’anta sun damke wasu matasa da ake zargin bata-gari ne dauke muggan makamai a karkashin gadar Dangi da ke jihar.
KAROTA ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinta, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya raba wa manema labarai a yau Talata.
- Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Da Nadin Ariwoola A Matsayin Alkalin Alkalai Na Kasa
- ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidaje Da Dama A Kaduna, Suna Sace Jama’a
Sanarwar ta ce, jami’an sintiri na hukumar ne suka samu nasarar cafke matasan da daddare a karkashin gadar Dangi.
Haka kuma hukumar ta ce, guda daga cikin jami’anta da suka cafke wadanda ake zargin, mai suna Mas’ud Ya’u Yusuf ya ce, sun kama su ne lokacin da suka iske su suna kwance a karkashin gadar, inda suka same su da nau’ikan kayan shaye-shaye da makamai.
Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun fada wa hukumar cewa kwanansu hudu da shigowa garin Kano daga jihohin Katsina da Zamfara.
Hukumar ta ce, bayan kammala bincike ta mika matasan ga rundunar ‘yan sandan don fadada bincike tare da daukar mataki na gaba.
Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan’agundi ya yaba da kokarin jami’an, sannan ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsi na wadansu mutane da ba su yarda da su ba domin tabbatar da tsaron unguwanni da ma jihar Kano baki daya.