Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta (NSCDC), sun cafke barayin wayar wutar lantarki a karamar hukumar Kura da ke jihar Kano.
Kwamandan rundunar a Kano, Adamu Idris Zakari, ne ya bayyana hakan yayin zanta wa da manema labarai a yau Talata.
- Buhari Ya Sayar Da NNPC, Ya Kaddamar Da Sabon Kamfanin Mai Na Kasa
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 9 A Katsina
Zakari ya ce an kama Surajo Tanimu da Ghali Ali da dauri-dauri na wayoyin wutar lantarkin, kirar ‘Armo’ mai kimanin tsahon mita 8, wacce darajarta ta kai kimanin Naira miliyan daya.
Ya ce, kamen ya biyo bayan bayanan sirri da korafi da suke samu daga mahukuntan vabban asibitin Kura game da sace-sacen kayan wutar lantarki ake musu a yankin.
Bayanai sun ce, sakamakon wannan ne, rundunar ta samu nasarar kama wasu su biyu.
“Mun fara bincike, kuma muna masu tabbatar wa da al’umma za mu samo wadannan masu laifi domin gurfanar da su a kotu,” a cewar Kwamanda Zakari.