Jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da mutane 84 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ‘yan ta’adda 3 a wani gagarumin farmaki da sojojin hadin gwiwa suka kai a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasir Mua’zu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sojoji na 17 Birget tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama ta ‘Operation Forest Sanity’ ne suka kai farmakin.
- Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Bisa Daidaito Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Amfanar Da Kamfanonin Duniya
- Waiwaye: Jihohin Da Aka Taɓa Sanya Dokar Ta-ɓaci A Nijeriya
Mua’zu ya ce, an kai harin ne a kan fitacciyar maboyar ‘yan ta’adda a karkashin jagorancin Sanusi Dutsin-Ma a tsaunukan Pauwa.
A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan.
Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka.
Bayan haka, sojojin sun ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza bakwai, mata 23, da kananan yara 54 da aka tsare a sansanonin ‘yan ta’addan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp