Sojojin Operation Fansan Yanma tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai sun daƙile wani sabon harin ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.
Sun ƙwato bindigogi guda uku ƙirar AK-47 daga hannun maharan.
- Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
- Yanzu-yanzu: WAEC Ta Rufe Shafin Duba Jarabawar WASSCE 2025
Wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ne ya bayyana wannan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.
Rahoton ya ce harin ya faru ne da safiyar ranar Laraba a wani daji da ke gabashin Tsafe, kusa da garin Yankuzo.
‘Yan bindigar na ƙoƙarin shiga garin ne ta wani ɓangare na daji kafin jami’an tsaro su tare su.
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar.
Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu.
‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi ba tukuna.
Bayan faɗan ta yi tsanani, an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin ci gaba da matsa wa ‘an bindigar da suka tsere lamba tare da hana su sake kai hari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp