Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fuskanci tsaiko a safiyar Alhamis, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Sanatan ta fuskaci tsaiko yayin da ta ke shirye-shiryen shiga jirgin British Airways zuwa birnin Landan tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan, lokacin da jami’an hukumar shige da fice suka dakatar da ita.
- Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
- EFCC Ta Kama Ɗaliban BUK 25 Kan Zargin Aikata Damfara A Intanet A Kano
Jami’an sun karɓe fasfon ɗinta inda suka ce tana da “barazana ga tsaron ƙasa.”
Wannan ya haifar da ruɗani a filin jirgin.
Ganau sun ce Sanata Natasha ta kasance cikin natsuwa kuma ta bayyana wa jami’an cewa babu wata doka da ta ba su ikon karɓe mata fasfo.
Ta ce: “Kotu ba ta bayar da umarni ba? Ba ku da ikon karɓe fasfona.”
Ba a bayyana wata hujja ko dalili a hukumance ba kan dalilin karɓe fasfo ɗin nata ba, lamarin da ya sa wasu suka zargi cewa ana shirya mata maƙarƙashiya irin ta siyasa.
An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana kiran waya cikin sauri yayin da lamarin ya ɗauki lokaci.
Bayan ‘yan mintuna, jami’an sun mayar mata da fasfo ɗin ba tare da wani bayani ba.
An bar ta ta shiga jirgin kafin ya tashi.
Wasu daga cikin fasinjojin da suka shaida lamarin sun bayyana abin a matsayin abin kunya, inda suke kallon lamarin a matsayin amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.
Har yanzu, hukumar shige da fice ta ƙasa da ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ba su ce komai ba game da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp