Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kashe wani kwamandan ‘yan bindiga da aka fi sani da Dogo Maikasuwa a wani kazamin artabu da jami’an tsaro suka yi.
A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Dogo Maikasuwa wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion’ ya jagoranci hare-hare da sace-sacen jama’a da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma kananan hukumomin Chikun da Kajuru a jihar.
- Matakai 20 Na Kandagarki Da Shawo Kan Cutar COVID-19 Za Su Inganta Zirga-zirgar Al’umma Da Zuba Jari A Kasar Sin
- Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin G20 Da Na APEC Tare Kuma Da Ziyara A Thailand
Sanarwar ta bayyana Dogo a matsayin daya daga cikin ‘yan ta’adda mafi gawurta da ke jagorantar sauran al’umma wajen ta’addanci a jihar.
Aruwan ya kara da cewa, Dogo ya jagoranci ‘yan bindiga nasa wajen aikata ta’asa da muguwar dabi’a, inda sukan kashe wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da aka jinkirta kai musu kudin fansa.
Aruwan, ya ce sauran ‘yan bindigar sun tsere da raunukan bindiga.
“An kuma tattaro cewa daya daga cikinsu ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wannan kazamin artabun.
“An bayyana wannan ci gaban ne a wani martani da jami’an tsaro suka kai.
“A cewar majiyoyin leken asiri, ko da yaushe yana sanye da kakin soji sannan dauke da bindiga kirar AK47. Irin wannan bayyanar da ya yi ne a artabunsa da jami’an tsaro aka kashe shi,” in ji Aruwan.
Ya kara da cewa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya samu jawabai na jami’an tsaro tare da godiya tare da yabawa jami’an da suka jagoranci aikin yaki da ‘yan bindigar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp