An kubutar da wata lauya Barista Rukayyat Mustafa da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita a ranar Lahadi a Sakkwato.
Rundunar ‘yansanda tare da sojoji da ‘yan banga ne suka ceto Rukayyat a ranar Laraba tare da wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su.
- ‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu
- Rikicin Masarautar Kano: Lauyoyi Da Alƙalai Sun Tozarta Ɓangaren Shari’a – Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi
Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar, Kwamishinan ‘yansandan Jihar Sakkwato, CP Hayatu Kaigama ya ce, “A ranar 26/05/2024 da misalin karfe 02:30 na dare, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a yankin Badon Runji a jihar inda suka yi garkuwa da Barista Rukayya Mustapha da wani Salim Abdulsalam.
“A ranar 29/05/2024 jami’an ’yansanda daga sashin Yabo tare da hadin gwiwar sojoji da ’yanbanga da ke aiki da rahoton sirri suka farmaki ‘yan bindigar.
“Farmakin wanda aka kai a yankin Binji, ya yi sanadin kubutar da mutane uku tare da bindige daya daga cikin ‘yan bindigar yayin da sauran suka arce da raunin bindiga” in ji CP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp