Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow, wadanda ke fafutukar ganin an sako shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.
Masu zanga-zangar sun tsere daga taron nasu ne bayan hadin gwiwar jami’an tsaro sun fara fito fa harsasai na kisa.
Masu zanga-zangar karkashin jagorancin mai kungiyar #RevolutionNow kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, sun taru ne da misalin karfe 6:50 na safe a kusa da hedkwatar ma’aikatar harkokin mata da ke gundumar tsakiyar birnin tarayya.
Gamayyar Jami’an tsaron sun hada da Rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF) da Guards Brigade, DSS da NSCDC, inda suka tsaurara matakan tsaro a kusa da fadar shugaban kasa, tun ranar Lahadi.
Sun kafa shingaye a manyan hanyoyin da suka kai ga fadar shugaban kasa (Villa), Majalisar Dokoki ta kasa, hedikwatar Kotun daukaka kara, hedikwatar sojoji da kuma dandalin taro na Eagle Square.














