Hukumar gudanarwar Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoko (UDUS) ta bayyana cewa harin da ya faru a yammacin ranar Lahadin da ta gabata a harabar jami’ar, lamarin na fashi ne ba na ‘yan bindiga ba.
Sabanin labaran da ke yawo, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Lawal Bilbis, a wani taron manema labarai a ofishinsa a ranar Talata, ya ce harin na fashi ne, ba wai harin ‘yan bindiga ba.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Kansila A Katsina
- ‘Yan Kasuwa 40 Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Kebbi
Farfesa Bilbis, ya yi kira ga al’ummar Jami’ar da kuma iyaye da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa “babu wani abin damuwa game da tsaron rayukan daliban jami’ar.
“Bari da farko na yaba da zuwanku domin tantance hakikanin abin da ya faru a Jami’ar domin kawar da tashe-tashen hankulan da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta.
“Jami’an tsaro a makarantar ne suka sanar da ni wani abu da ya faru, lokacin da na isa Karamar Hukumar da abin ya faru da misalin karfe 11:00 na daren jiya, sai aka ga lamari ne da ya shafi fashi ba wai na ‘yan bindiga ba.
“Sun dauki kwali biyu na lemon sha na Maltina da wayoyi takwas na dalibai wadanda akai cajin su wani shago.
“Nan take na sanar da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sandan Nijeriya, jami’an NSCDC kuma dukkansu sun mayar da martani ta hanyar tura mutanensu wurin.”
Mataimakin shugaban jami’ar ya kara yaba wa jami’an tsaro bisa tura mutanensu cikin gaggauwa wurin da lamarin ya faru.