Jami’ar tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina (FUDMA) ta kara fadawa cikin wata rigimar zaben shugabanci biyo bayan tashe-tashe hankula kan wanda zai shugabanci jami’ar.
Tashe-tashen hankulan ya gudana ne bayan da zauran majalisar gudanarwa na jami’ar yayin fid da sunayen ‘yan takarar domin yi masu jarabawar gwaji kan mukamin shugabancin makarantar.
- FUDMA Za Ta Karrama Sarkin Bichi, Sarkin Daura Da Tsohon Gwamnan Katsina
- Shugaban Jami’ar FUDMA Ya Zargi Wasu Ma’aikatan Jami’ar da Taimakawa Ƴan Bindiga
Wasu ‘yan takarar sun soki tsarin yadda ake gudanar da tantancewar, suna masu sukar shugaban mai barin gado, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi kan yin ruwa da tsaki wajen yadda ake gudanar da aikin domin goya wa dan takararsa baya.
Zarge-zargen sun jawo cece-kuce kan lamarin, musamman tsakanin malaman makarantar, inda wasu ‘yan takara guda biyu suka rubuta kara suna kalubalantar yadda ake gudanar da jarabawar tantancewar.
Daya daga cikin ‘yan takarar, Farfesa Sadik Radda ya gabatar da kara zuwa ga ministan ilimi, Dakhtaa Tunji Alausa yana mai zargin cewa ana kokarin hada kai domin cire shi daga cikin ‘yan takara.
Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar.
Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kamar yadda doka ta tanada.
Dukkan ‘yan takarar sun bayyana gamsuwarsu kan shigowar gwamnatin tarayya cikin lamarin, inda suke yi kira ga ministan ilimi ya sake duba dukkan matakan da da aka bi domin yin gaskiya kamar yadda dokar makarantar ta tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp