Gamayyar rukunin jami’o’in MAAUN ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwar kasa da kasa da ‘Seneca College of Applied Arts and Technology’ da ke kasar Canada, wacce aka tabbatar da wannan alaka ta hanyar rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin inganta koyar da harshen Turanci, musayar dalibai, da hadin gwiwa na tsare-tsaren ilimi.
Rukunin MAAUN, wanda ya kunshi Jami’ar ‘Canadian University of Nigeria’ da ke Abuja, Franco British International University da ke Kaduna, Maryam Abacha American University da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar, da Maryam Abacha American University da ke Kano, na neman fadada tasirinta a duniya ta hanyar wannan hadin gwiwar.
- Jagororin Tsaro Da Na Sojoji Daga Sama Da Kasashe 100 Za Su Halarci Taro Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Beijing
- INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025, inda Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya kafa kuma Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN, ya wakilci jami’o’in guda hudu, a yayin da David Agnew ya sanya hannu a madadin Seneca College.
A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje.
“Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi.
A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin ilimi ga ma’aikatan MAAUN.
Haka kuma, yarjejeniyar ta tanadi shirye-shiryen kirkiro da karatun hadin gwiwa, inda za a tantance irin takardar shaidar da za a bayar, tsawon lokacin karatu, da kuma bangaren da shirin za a mayar da hankali wanda cibiyoyin biyu za su sahhale.
Bugu da kari, yarjejeniyar ta tanadi dabarun inganta damar samun ilimi a Seneca ga daliban da ke cikin rukunin jami’o’in MAAUN tare da wasu bangarori na hadin gwiwar da za a iya yi a nan gaba.
Farfesa Gwarzo ya nuna kwarin gwiwarsa game da dogon tasirin wannan hadin gwiwa, inda ya jaddada cewa yarjejeniyar za ta zama ginshiki wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa.
“Muna da niyyar aiwatar da wannan yarjejeniya cikin cikakken tsari domin bunkasa bincike da kirkire-kirkire tare da cimma manufofin da aka tsara. Wannan muhimmin mataki ne wajen karfafa ingancin ilimi a jami’o’inmu,” in ji shi.
Wannan yarjejeniyar na nuni da kokarin da gamayyar rukunin jami’o’in MAAUN ke yi na fadada hadin gwiwa da sauran cibiyoyi a duniya, domin tabbatar da cewa dalibai da ma’aikata sun amfana daga kwarewa da horo na kasa da kasa, tare da karfafa damar gudanar da bincike da kirkire-kirkire a rukunin jami’o’i.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp