Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) da ke Jihar Kano, ta umarci ɗalibanta mata da ke zaune a wasu ɗakunan haya guda biyu da su gaggauta barin wuraren nan take, saboda rahotannin aikata rashin ɗa’a.
Jami’ar ta ce ta soke amincewarta da Al-Ansar Indabo Female Students Hostels, bisa zarge-zargen aikata miyagun halaye, yanayin zama mara kyau da kuma karya ƙa’idodin jami’ar.
- Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Da Ake Iya Sarrafawa Daga Nesa
- Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
A wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ranar Lahadi, Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Rayuwar Ɗalibai, Dokta Hamza Garba, ya ce wannan mataki an ɗauke shi ne domin kare lafiyar ɗalibai da kuma tabbatar da ɗa’a a jami’ar.
Ya bayyana cewa jami’ar ta samu rahotanni kan abubuwa kamar rashin isasshen ruwa da wutar lantarki, tashin hankali tsakanin ɗalibai, shiga da fice ba tare da izini ba cikin dare, da kuma zaman mutanen da ba a san su ba a ɗakunan.
“Wannan matsaloli suna barazana ga lafiyar ɗalibanmu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki.
Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa.
Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba.
Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp