Babbar sakatariyar taron cinikayya da raya kasa ta MDD (UNCTAD) Rebeca Grynspan ta bayyana cewa, bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) wuri ne na hada ra’ayoyi, da al’adu, baya ga zama wani sabon salo na raya ayyukan hadin gwiwar kasa da kasa.
Jami’ar wadda ta bayyana a yayin bikin bude baje kolin na CIIE karo na shida, wanda zai gudana daga yau Lahadi zuwa Juma’a, ta bayyana cewa, bikin CIIE, a matsayin dandalin musayar ra’ayi mai karfi, ya nuna aniyar kasar Sin ta daidaita huldar cinikayya da kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa, da kanana da matsakaitan masana’antu. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp