Wakilin kasar Sin kan harkokin cinikayya na kasa da kasa, kuma mataimakin ministan harkokin cinikayyar kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana yau Jumma’a a taron manema labarai cewa, kasar Sin a shirye take ta shiga tattaunawa, da fadada bangarorin hadin gwiwa, da daidaita bambance-bambance tsakaninta da kasar Amurka, domin sa kaimi ga inganta bunkasuwar dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa tsakanin kasashen biyu, bisa mutunta juna, da zaman lafiya da hadin gwiwar samun nasara tare.
Wang ya kara da cewa, tarihi ya nuna cewa, kara haraji kan kayayyakin kasar Sin ba zai iya warware gibin cinikayyar kasar da ke kakaba harajin ba, a maimakon haka, yana haifar da tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma hauhawar farashin kayayyaki, inda daga karshe nauyin yake komawa kan masu sayayya. (Yahaya)