Babban jami’in ofishin jami’ar zaman lafiya na MDD wato UPEACE dake birnin Geneva David Fernandez Puyana, ya bayyana cewa, shawarar inganta jagorancin duniya ta GGI da kasar Sin ta gabatar a yayin bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD ta zo a daidai lokacin da ya dace, kuma za ta jagoranci duniya zuwa ga samun makoma mai kyau mai cike da adalci da dimbin basira.
A cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, Puyana ya bayyana cewa, shawarar da kasar Sin ta gabatar ta inganta jagorancin duniya wata murya ce mai asali da ke cikin yarjejeniyar kafuwar MDD, kasancewar ta tabbatar da goyon bayan muhimman ka’idojin da suka shafi tsarin kasa da kasa da aka kafa a shekarar 1945, wato hadin gwiwa, da tattaunawa, da mutunta ikon kasa, da kuma tsarin da aka gina bisa dokokin kasa da kasa.
A cewar Puyana, shawarar ta yi amfani da hangen nesa a matsakaici da kuma dogon lokaci, inda ta ba da mafita ga dimbin kalubalen duniya da har yanzu ba a warware ba, tare da karfafa gina ingantaccen tsarin jagorancin duniya bisa adalci. A sa’i daya kuma, ta nuna muhimmancin bunkasa tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya, inda hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), wadda kasar Sin ta dade tana goyon bayanta, take taka rawar gani sosai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp