An shiga rudani a Jihar Zamfara yayin da wani jami’in tsaro, ya bindige wani mutum da ke sallar Idi har lahira, bisa kuskure a jihar.
Nan take wasu fusatattun matasa suka far wa jami’in tsaron, wanda ke aiki da hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence.
- Gidauniyar Saraki Ta Kammala Shirin Rabon Abincin Buda-baki
- Dalilin Haramta Tafiyar Dare A Iyakokinmu Da Katsina Da Sokoto – Gwamnatin Zamfara
An ruwaito wanda jami’in ya yi harbin ne a lokacin da ya ke kokarin cafke wani bata-gari.
Lamarin da faru ne yayin sallar Idi a Gusau, lamarin da ya fusata al’umma tare da haddasa rudani a yankin, inda har fusatattun matasa suka banka wa motar Civil Defence wuta.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kama jami’an da ke da hannu a lamarin.
Sai dai mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya a jihar, Ikor Oche, ya musanta zargin cewa jami’an Civil Defence ne suka yi harbe mutumin.
Oche ya ce hukumar NSCDC ta kaddamar da bincike don gano ainihin abin da ya faru.
A gefe guda kuma gwamnatin jihar, ta bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da bincike don yin adalci.