Mataimakin babban sakataren nazari kan manufofi da daidaitawa da tsara shirin ci gaba a ofishin shugaban kasar Zimbabwe da majalisar ministocin kasar, Willard Manungo, a ranar Juma’a ya yabawa kamfanin karafa na kasar Sin wato Dinson Iron and Steel Company (DISCO) bisa goyon bayan da yake baiwa kokarin kungiyar raya yankunan kudancin Afirka ko SADC kan bunkasa masana’antu.
Hadaddiyar masana’antar sarrafa karafa da aka kafa a lardin Midlands na Zimbabwe ba wai kawai zai kara bunkasa masana’antu a Zimbabwe ba, har ma a yankin kudancin Afirka baki daya, a cewar Willard Manungo.
- Tsadar Rayuwa: Atiku Ya Yi Allah Wadai Da Harbin Masu Zanga-zanga
- Gwamnati Ta Bai Wa Gwamnoni Fiye Da Naira Biliyan 570 Don Tallafa Wa Talakawa – Tinubu
Ya bayyana haka a rangadin aiki da ya yi a wannan masana’antar sarrafa karafa tare da wakilan gida da waje da suka halarci taron raya masana’antu na SADC da aka kammala a ranar Juma’a a birnin Harare na Zimbabwe, inda kuma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babban aikin zai farfado da karfin tattalin arziki da masana’antu na Zimbabwe, da kungiyar ta SADC da kuma nahiyar Afrika baki daya.
Har ila yau, ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasar Zimbabwe ta yi koyi da kwarewar kamfanin Dinson, ta kuma yi amfani da wannan tsari, wajen samun karin jarin kasar Sin a sauran sassan tattalin arziki, kamar masana’antun noma, don bunkasa ayyukanta. (Yahaya)