Jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Yobe, inda ta lashe dukkan kujerun shugabanni da kansiloli. Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman kanta ta Jihar Yobe Dakta Mamman Muhammad ne ya sanar da sakamako a shelƙwatar hukumar da ke Damaturu a yau Lahadin.
Zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar, ya nuna tasirin jam’iyyar a jihar, domin duk wata kujera da aka yi takara a zaɓukan ƙananan hukumomi ƴan takarar jam’iyyar APC suka lashe. Kana kuma yana nuni da irin ƙalubalen da ke gaban jam’iyyun adawa kafin su iya amshi ragamar jihar.
- Jihar Yobe Ta Kashe Naira Miliyan ₦179 Wajen Tallafawa Mahajjata 1,332
- Jihar Yobe Ta Kashe Naira Miliyan ₦179 Wajen Tallafawa Mahajjata 1,332
Duk da ana ta kira a mayar da zaben ƙannanan hukumomi ya koma ƙarƙashin gwamnatin tarayya sakamakon zargin danniya da ake yi gami da magudi ga jam’iyyun adawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp