Daga jiya Asabar har zuwa gobe Litinin, al’ummar kasar Sin na gudanar da hutun kwanaki 3, domin bikin gargajiya na Duanwu, ko kuma “Dragon Boat Festival” a harshen Turanci, wanda ya sa kaimi ga bangaren yawon shakatawa na kasar Sin.
Bisa alkaluman da kamfanin Ctrip, mai samar da hidimomin yawon shakatawa na kasar Sin ya fitar, an ce a lokacin bikin Duanwu, yawan mutanen kasar Sin da suka yi odar dakunan otel, da tikitin zirga-zirga ta kamfanin, ya karu da kashi 20%, kan na makamancin lokaci na bara.
A nasa bangare, kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin, ya sanar da cewa, ana sa ran ganin zirga-zirgar mutane kimanin miliyan 74 ta jirgen kasa a kasar Sin, tsakanin ranar Juma’a zuwa Talata mai zuwa. (Bello Wang)