Shugaban jam’iyyar APC a jihar Neja, Hon. Haliru Jikantoro, ya umarci ruguza kungiyoyin yakin zaben ‘yan takara da aka kafa kafin lokacin yakin neman zaben fidda-gwani, jam’iyyar ta umarci a bin tsarin dokar hukumar zabe ta kasa.
Jami’in yada labaran jam’iyyar, Hon. Musa D. Sarkikaji ne ya bada nasarwar yammacin yau juma’a.
- 2023: INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zabe A Karshen Watan Yuli
- 2023: Muna Fata APC Ta Dawo Mulki A Jihar Bauchi -Kwamared Sabo
Shugaban ya ce dukkanin kungiyoyin da aka zaba sh bi tsarin jam’iyya ne wajen kafa gangamin yakin neman zaben ‘yan takara a dukkanin kananan hukumomi 25 na jihar.
Ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da suka kafa kungiyoyin yakin neman zaben ‘yan takara da su yi rajista da jam’iyya do samun damar tallata dan takarar jam’iyya.
Hon. Jikantoro ya ce jam’iyya na jiran umarnin hukumar zabe na fara yakin zabe da hanin ta ga jam’iyyu na fara yakin zabe, ya shawarci ‘ya’yan jam’iyyar da su zama masu bin umarni wajen bin dokokin don samar da tsari mai inganci don samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.