Jam’iyyar Labour Party (LP) ta yi watsi da hukuncin da kotu ta yanke na soke zababbun mambobinta ciki har da zababben gwamnan Jihar Abia, Dakta Alex Otti.
A sanarwar da mai rikon babban Sakataren watsa labarai na jam’iyyar, Obiorah Ifoh, ya fitar ya bayyana cewa hukuncin ya matukar basu mamaki.
- Karin Bayani: Kurar Da Ta Biyo Bayan Rushe Nasarar Zababben Gwamnan Abia
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
Jam’iyyar ta nuna damuwarta kan hukuncin da Alkalin kotun Mai Shari’a M.N Yanusa, na kotun tarayya da ke Kano ya yi na kan karar da dakatattun mambobin jam’iyyar masu biyayya ga tsagin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Lamidi Apapa, suka gabatar masa.
Jam’iyyar ta ce, bata san da wata karar da aka shigar da ita a Kano ba, domin ba a ba su kwafin sanarwar karar ba balle su son da Shari’ar ba.
Tsohon mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Samuel Akingbade Oyelekan, ya jima da barin wannan ofis din nasa domin ya gabatar da kansa a kashin kansa ba tare da amincewar shugabancin jam’iyyar ba.