Jam’iyyar Labour (LP) ta fuskanci babban koma baya sakamakon ficewar wasu ‘yan majalisa guda biyar daga cikinta, suka kuma sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a yau Alhamis.
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai Tochukwu Okere (Imo), da Donatus Mathew (Kaduna), a Bassey Akiba (Cross River), da Iyawe Esosa (Edo) da kuma Daulyop daga Filato
An tabbatar da sauya sheƙar tasu ne a lokacin zama na majalisa, inda Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙun sauya shekarsu a gaban taron.
- Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters
- Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido
Donatus Mathew, wanda ke wakiltar Kaura a Kaduna, ya bayyana dalilinsa na barin jam’iyyar LP a matsayin matakin kashin kai. Ya ce, ko da yake wannan shawara ba za ta yi wa dukkanin waɗanda suka zabe shi daɗi ba, amma wani yanayi ne domin alfanunsu.