Jiya Lahadi ne aka rufe taron tattaunawar Shangri-La karo na 19 a kasar Singapore, inda firaministan kasar Japan Fumio Kishida ya yi jawabi, wanda a cewar kafofin yada labaru na Japan, bai koye yunkurinsa na yin fito-na-fito da kasar Sin a fannonin aikin soja, tattalin arziki da ma dukkan sauran fannoni ba.
Wannan shi ne karo na 2 da firaministan Japan ya yi jawabi a taron tattaunawar Shangri-La. A jawabin Kishida ya yi ikirarin yin fito-na-fito da kasar Sin ta fuskar siyasa, aikin soja, da tattalin arziki, kana ya yi shelar kara yawan kudaden da kasar za ta kashe a fannin aikin soja, tare da ingiza sauran kasashen Asiya da su yi fito-na-fito da Sin.
Amma Japan ba ta cimma burinta ba. Ministan tsaron kasar Indonesia Prabowo Subianto ya nuna cewa, kasarsa tana mutunta dukkan manyan kasashe, don haka ba ta shirya shiga kawancen sojan ba. Babban ministan kasar Malaysia kuma ministan tsaron kasar Hishammuddin Hussein ya jaddada cikin jawabinsa cewa, kungiyar ASEAN za ta zabi hanyarta da kanta.
Mafi yawancin kasashen Asiya sun mayar da bunkasar kasar Sin a matsayin kyakkyawar dama, a maimakon barazana.
Don haka ‘yan siyasan Japan, ba za su iya rusa alakar dake tsakaninsu da kasar Sin ba. Yadda suke bauta wa Amurka ya sake nuna ainihin nufinsu, ya kuma yi mummunar illa kan tsari da odar kasa da kasa da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali a yanki. (Tasallah Yuan)