Kasar Japan, ta bai wa Nijeriya bashin dala miliyan 108 a matsayin daukin gaggaka don samar da abinci a kasar.
Jakadar Kasar Japan, Yuka Furutani da ke ofishin Jakadancin kasar a nan Nijeriya ce ta sanar da hakan; a wani taron bita da aka shirya wa wasu malaman aikin gona ta hanyar fasahar zamani, wadda aka gudanar a Abuja.
- Ya Kamata Tuba Daga Laifin Yaki Da Tsoffin Sojojin Japan Ke Yi Ya Zama Matsaya Guda Ta Daukacin ‘Yan Siyasar Japan
- Da Alamu Japan Ta Shirya Gyara Kuskurenta
Hukumar Aikin Noma ta Afirka da ke bayar da shawara a fannin aikin noma (AFAAS), tare da hadin gwiwar Kungiyar Aikin Noma ta Afirka Sasakawa da Cibiyar Aikin Noma ta Kimiyya (AGRA), da kamfanin tuntuba na Sahel da kuma shirin Aikin Noma na Afirka ne suka shirya taron a kwanakin baya.
Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce, ta dauki nauyin shirin; wanda aka gudanar a Jihohin Oyo, Gombe da kuma Kaduna.
A cewar Furutani, Gwamnatin Kasar Japan; na ci gaba da mayar da hankali wajen sama wa kasasehn Afirka da ke fama da karancin abinci bashi.
Ta sanar da cewa, a watan Afirilun 2024; Nijeriya da Japan, sun rabbata hannun yarjejeniya a wani taro na kasa da kasa da aka gudanar a Tokyo kan yadda Japan za ta samar da bashin dala miliyan 108 ga Nijeriya.
Kazalika, ta bayyana cewa; Japan ta kara fadada wannan bashin zuwa akalla dala miliyan 4.2, domin kara habaka samar da Irin noman Shinkafa a Nijeriya.
A nasa jawabin, Daraktan Kungiyar Aikin Noma ta Afirka Sasakawa da ke Nijeriya, Godwin Atser wanda ke jagorantar aikin ya bayyana cewa; Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce, ta zuba makudan kudade; don gudanar da aikin, wanda kuma za a gudanar da bincike a Jihohin Oyo, Gombe da kuma Kaduna.
Godwin ya sanar da cewa, za a gudanar da binciken ne; domin gano adadi da kuma malaman aikin gona, musamman don lalubo mafitar da ake bukata ta bai wa kowane jinsi damar duba sauyin noma a Nijeriya, musamman a kan amfanin gona na Masara, Farin Wake, Rogo, Waken Suya da kuma a fannin dabbobi.
Muna da manhajar fasahar zamani iri-iri da aka samar da za iya amfani da su, don jawo manoma a jiki tare da ba su kariyar da ta dace”, in ji shi.
Godwin ya kuma yi nuni da cewa, idan aka kara habaka noma; hakan na nuna cewa, an tunkari turbar rage talauci a cikin al’umma, musamman duba da cewa; kashi 70 cikin 100 na a’lummar da ke zaune a karkara, sun dogara ne da fannin aikin noma.
Shi kuwa, Deola-Tayo Lordbanjou; Darakta a Hukumar Kula Bunkasa Ayyukan Malaman Aikin Gona ta Tarayya ya sanar da cewa, bisa wani bincike da aka gudanar, an gano cewa; akwai karancin ilimantarwa a fannin aikin noma a Nijeriya.
Deola-Tayo ya kara da cewa, malaman aikin gona sun fi yawa a shekarar 1980 a kasar, idan aka kwatanta da wadanda ake da su yanzu a fadin wannan kasa.