Masana a Jami’ar Tokyo da ke Kasar Japan, sun kirkiro wata sabuwar fasahar kimmiyar zamani da za ta taimaka wa masu kiwon Shanu wajen samar da Madara mai inganci tare da wadatarta, wadda ke dauke da kyamarorin da za su rika hango dakunan kwanan Shanun.
Mataimaki a Sashen Samar da Bayanai da Fasahar Kimiyyar Kwamfuta na Jami’ar, Farfesa Yota Yamamoto ne ya jagoranci tawagar.
- CICPE Karo Na 5 Zai Mayar Da Hankali Kan Kirkire-Kirkiren Fasahohin Zamani
- Nan Ba Da Jimawa Ba Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ƙirar Nijeriya Zai Fara Tashi – NASENI
Sauran ‘yan tawagar sun hada da Mista Kazuhiro Akizawa, Mista Shunpei Aou da kuma Farfesa Yukinobu Taniguchi.
Har ila yau, an wallafa wannan bincike ne a wannan shekara ta 2025 da muke ciki.
A cikin wata sanarwar da wani mai bincike Rishita Sachan ya fitar a madadin tawagar hudda da jama’a na jami’ar ta ce, sabuwar kimiyyar za ta kuma taimaka wajen ingnata kiwon lafiyar Shanun da samar da wadatacciyar Madara
Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu.
Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar Madarar Shanu a kasar nan.
Ana dai ci gaba da bukatar ingantacciyar Madarar Shanun a fadin wannan kasa, sai dai ana ci gaba da fuskantar kalubalen lafiyayyun Shanun, musamman a kasa irin Nijeriya.
Sabuwar kimiyyar za ta bayar da damar saurin sanya ido kan yadda kiwon lafiyarsu ke tafiya, saurin gano ko sun harbu da wata kwayar cuta da kuma kula da lokacin nakudanarsu.
“Wannan kimiyyar gwaji ne na farko, na sabuwar kimiyyar wadda za ta taimaka wa masu kiwon Shanunun hango daukacin dakunan kwanan Shanun da suke kiwatawa”, in ji Farfesan.
Yamamoto ya kara da cewa, wannan kimiyyar za taimaka wa masu kiwon wajen gano yanayin kiwon lafiyar Shanun da kuma samar da ingantacciyar Madarar Shanu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp