Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce daga jerin sanarwa dake fitowa, ana iya fahimtar yadda da gangan, bangaren Japan ke ci gaba da raba-kafa, tare da kaucewa muhimman batutuwa da ba kai ga warwarewa ba a batun yankin Taiwan na Sin, a wani yunkuri na karkatar da tunanin jama’a, da kaucewa daukar nauyin da ya rataya a wuyanta.
Guo, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da aka yi masa tambaya game da zargi, da sukar tsarin tsaron Sin, da aka jiyo ministan tsaron Japan Shinjiro Koizum na yi. Game da hakan, Guo ya ce Sin na matukar adawa da kalaman ministan na Japan. Kazalika, a matsayin Japan na kasa wadda a tarihi ta aikata danniya, ba ta cancanci furta wasu kalamai dangane da tsarin tsaron kasa na Sin ba. (Saminu Alhassan)














