Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan wani rahoto da jaridar Daily Trust da ta wallafa a ranar Litinin game da kamun bakin ludayin gwamnatin shugaba Buhari.
Gundarin rahoton ya mayar da hankali ne kan ikirarin cewar tun hawa kan karagar mulkin APC mai mulki babu abin da ya sauya a Nijeriya.
- Mataimaki: Gwamnonin APC Na Alfahari Da Zabin Tinubu – Bagudu
- Na Matsu Mulkina Ya Kare Na Sauka – Buhari
Amma a martanin da fadar shugaban kasa ta yi a ranar Litinin ta hannun, Malam Garba Shehu, ta ce ba daidai bane hasashen rahoton da suka yi ba, musamman wajen fadakar da alummar kasar.
A cewar sanarwar rahoton cin fuska ne kai tsaye ga shirye-shiryen da gwamnatin Buhari ta kirkiro kamar na tsarin fallasa barayin gwamnati ga ‘yan Nijeriya, inda sanarwar ta kara da cewa, dole ne a jinjina wa gwamnatin kan irin kokarinta.
Sanarwar ta ce, marubutan sun yi gaskiya ganin yadda suka ce, a cikin rahoton ita ma Nijeriya kamar sauran takwarorinta kasashen duniya na fuskantar matsin tattalin arziki.
A cewar sanarwar, “A yau Nijeriya ta ci gaba fiye da yadda gwamnatin shugaba Buhari ya iske ta, mussaman wajen bunkasa tattalin arziki Nijeriya, kokarin magance kalubalen rashin tsaro da yakar cin hanci da rashawa, abin sai dai ace, Allah san barka.”
Sanarwar ta buga misali da da cewa, “A 2015 Boko Haram sun kwace wasu yankuna a Arewa Maso Gabas amma gwamnatin Buhari ta kwato su, haka a watan Maris dakarun soji sun aika da jagoran ISWAP zuwa barzahu ta hanyar luguden wuta da jiragen yaki da gwamnatin ta sayo daga Amurka.
“Gwamnatin Buhari a tarihin Nijeriya ita ce ta farko da ta wanzar da mafita kan rikicin manoma da Fulani da Makiyaya ta hanyar kafa tsarin inganta kiwo na zamani na kasa (NLTP), wanda tuni aka kakkafa guraren yin kiwo na zamani, inda wannan ya taimaka matuka wajen rage yawan rikice-rikicen a tsakaninsu.
“Ita kanta Daily Trust, ta amfana da canjin shugabancin da Buhari ya samar, musamman wajen sha’anin tsaro domin a 2015 kofar shiga harabar Jaridar Daily Trust cike take da shingle da jami’an tsaro don gujewa harin ‘yan ta’adda amma a cikin shekaru bakwai na shugaba Buhari sun cire shingen.
“Gwamnatin Buhari ta karbo dubban miliyoyin kudaden gwamnati da wasu ‘yan Nijeriya suka wawure suka kai ketare wadanda kuma ta yi amfani da su don inganta rayuwar ‘yan kasar tare da zuba wasu kai tsaye, wajen dakile yaduwar annobar Korona ta hanyar tallafa wa talakawa da gyaran wasu hanyoyi da aikin jirgin kasa da kuma inganta wutar Lantarki.
“Kokarin da gwamnatin ke ci gaba da yi na kara sanya wa ta na ci gaba da samun aminta daga gun abokan huldarta na waje musamman wajen yakar cin hanci da rashawa, inda gwamnatin ta kirkiro da tsarin tara kudade a asusu na bai daya tare da karfafa ofishin Akanta-Janar na kasa don sa ido kan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati
“Gwamnatin ta samu nasara wajen dora fannin tattalin arziki a kan turba musamman ta hanyar samar da tsare-tsare, haka ta yi kokari wajen kaucewa fadawar kasar a cikin barazar karancin abinci da ya tura wasu kasashe bango, gwamnatin ta kuma kafa shirin haramta shigo da shinkafa daga ketare, inda wannan ya ba ta damar adana Dalar abinci miliyan biyar.
“Mun samar da Dalar shinkafa da dama a wasu jihohin kamar su Kebbi, Abuja, Neja, Gombe da kuma jihar Ekiti”.
A cewar sanarwar, an kara samun kakkafa manyan masana’antun sarrafa Shinkafa 54 tare da kakkafa kanana 1,000 da kuma farafado da masana’antun sarrafa takin zamani 57, inda sanarwar ta kara da da cewa kimamin marasa karfi miliyan 20 ne suka amfana da tallafin kudade ta hanyar tura masu daga bankuna, gwamnatin ta kirkiro da ciyar da ‘yan makaranta da sauransu kafa shirin.
A kashe, sanarwar ta ce, a irin wannan yanayin da kasar ke tunkarar zabubbuka, suka mai zafi ga gwamnati ta siyasa da sharhin ya yi, musamman a kan gwamnatin Buhari abu ne da ba a yi wa gwamnatin adalci ba.