Kudaden da aka zuba a bangaren harkokin sadarwa a Nijeriya, ya tashi daga dala biliyan 38 zuwa dala biliyan 77 a zango na biyu na shekarar 2023, kamar yadda Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Farfesa Umar Danbatta ya bayyana.
Danbatta, ya shaida hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a Kano karshen makon da ya gabata, ya ce, bangaren sadarwa ya ba da gudunmawar kaso 16 ga tattalin arzikin Nijeriya (GDP), a tsawon wannan lokacin.
Shugaban ya kara da cewa, Nijeriya na samun gagarumin ci gaba a wannan bangare na sadarwa kwarai da gaske ta fuskoki daban-daban, wanda hakan ne ya ba ta damar samun wannan tagomashi.