An bayyana jarin kasar Sin a matsayin wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Zimbabwe, tare da bayyana dimbin damarmakin kara zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren.
Da yake jawabi jiya Talata, yayin wani taron kara wa juna sani kan karfafa hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Zimbabwe a birnin Harare na kasar, Munetsi Madakufamba, babban daraktan cibiyar bincike da adana bayanai ta kudancin Afrika (SARDC), ya ce bayan kulla huldar diplomasiyya shekaru 45 da suka gabata, Zimbabwe da Sin sun samu ci gaba sosai a hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakaninsu.
Ya ce Zimbabwe tana zama muhimmin wurin zuba jarin kasar Sin a Afrika, inda Sin take amfani da jarin da fasaha da gogewa wajen lalubo tarin damarmakin hadin gwiwar tattalin arziki da taimakawa burikan kasar na samun ci gaba.
Ya kara da cewa, yayin da Zimbabwe ke neman farfado da tattalin arzikinta da zama kasa mai matsakaicin kudin shiga zuwa shekarar 2030, jarin kasar Sin zai iya taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa kokarin kasar na bunkasa ayyukan masana’antu da kirkiro gurabun ayyukan yi da inganta ci gaban tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp