Kasar Habasha dake yankin kahon Afirka, na cikin kasashen nahiyar Afirka dake kan gaba wajen cin gajiya daga jarin waje na kasar Sin, inda tuni kasar ta fara more manyan ababen more rayuwa da Sin ta gina karkashin shirye-shiryen raya kasa daban daban, ciki har da shawarar “ziri daya da hanya daya”, wadanda suka haifar da gagarumin sauyi a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.
Karkashin irin wadannan manufofi, a halin yanzu kasar Habasha na more ribar kyautatuwar sufurin jiragen kasa na zamani da kasar Sin ta gina, wadanda ke zirga-zirga cikin kasar da ma makwafciyar ta kasar Djibouti. Kuma hakan na zuwa ne a gabar da Habashan ke fatan samun karin jari daga sassa daban daban na kasar Sin.
Ko shakka babu irin yadda mahukuntan kasar Habasha ke bayyana kyakkyawan fata ga shigar karin jarin Sin cikin kasar, ya shaida gamsuwa da kasar ta yi da nasarorin da ta cimma bisa hadin gwiwarta da Sin.
Ga duk wanda ke bibbiyar ci gaban yankin kahon Afirka, yana iya shaida manyan nasarori da Habasha ta cimma a bangaren sufuri na zamani, da kafuwar yankin masana’antu na zamani, wanda ya baiwa kasar damar sarrafa hajoji da dama da ake amfani da su a cikin kasar da ma sauran kasashen Afirka.
A hakin yanzu kuma, Habasha na fatan kara fadada hadin gwiwa da sassan kasar Sin, wajen bunkasa harkokin sarrafa hajoji, da samar da makamashi mai tsafta, da inganta noma bisa dabarun zamani. A hannu guda kuma, kasar wadda ta zama a sahun gaba a Afirka wajen yawan cinikayya, da zuba jari tsakaninta da Sin cikin shekaru masu yawa da suka gabata, tana kuma amfani da wannan zarafi wajen bunkasa hada hadar fitar da hajojinta zuwa kasar Sin, da ma sauran sassan duniya masu yawa.
Tabbas sassan kasar Sin dake zuba jari a Habasha, sun taka rawar gani a fannin samar da guraben ayyukan yi, da bunkasa fasahohin wanzar da ci gaba, don haka ma masharhanta da dama ke ganin masu zuba jari na Sin a kasar Habasha, baya ga kasancewar su masu samar da kudade, sun kuma zamo muhimmin bangare na hadin gwiwar kasar, wajen warware kalubalen tattalin arziki da zamantakewa, duba da yadda suke taimakawa Habasha da jari kai tsaye, ba tare da la’akari da yawan riba ko gindaya wasu sharudda na siyasa ba.