Yayin da ake ci gaba da kirga asarori da rayukan da aka rasa sakamakon wata mummunar ambaliya da aka yi a birnin Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno, mutane da dama na nuna alhini da tausayawa ga wadannan mutane da abin ya shafa.
Daga cikin masu wannan jajantawa akwai jarumai a masana’antar Kannywood wadanda suka nuna alhini a bayyane suka kuma jajantawa gwamnati da kuma al’ummar jahar Borno.
- Sama Da Kasashe Da Hukumomin Kasa Da Kasa 70 Sun Ba Da Tabbacin Halartar Bikin CIIE Karo Na 7
- Zargin Yi Wa Almajiri Fyade: Masu Kare Hakkin Dan’adam Sun Sake Shigar Da Kara
Ali Nuhu
Daga cikin jaruman da suka jajanta wa al’ummar Jihar Borno akwai shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya kuma jarumi a masana’antar Kannywood Ali Nuhu Muhammad inda ya ce “Ina mika sakon jaje da kuma alhini ga mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a Jahar Borno da sauran yankunan kasar nan, Allah ya kawo mana saukin wannan al’amarin”.
Abba El Mustapha
Haka zalika akwai shugaban hukumar ta ce fina finai da dab’i na jahar Kano Abba El Mustapha shima ya jajantawa wadannan bayin Allah da ambaliyar ruwa ta shafa,a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook El Mustapha ya ce “Wallahi, da garin MAIDUGURI na Kwana na kuma tashi a raina. Ya Allah ka kawo musu mafuta ta ALHERI kasa IBTILA’IN da ya faru dasu ya zama kaffara”.
Sani Musa Danja
Akwai kuma jarumi kuma tsohon dan takarar shugaban karamar hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano Sani Musa Danja inda a wani faifan bidiyo da aka dora a shafukan zumunta ya ke cewa a madadin masana’antar Kannywood ya na jajantawa al’ummar birnin Maiduguri da ma jahar Borno baki daya, ya na fatan duk wadanda suka rasa dukiyoyins Allah ya mayar masu da mafificin alheri.
Aminu Ladan Abubakar (ALA)
Daya daga cikin dattawan mawaka a masana’antar Kannywood Aminu Ladan Abubakar wanda akafi sani da Ala shima ba a barshi a baya ba wajen jajantawa wadannan bayin Allah da iftila’in ruwa ya shafa,inda ya roki Allah ya gafarta wa wazanda suka rasa rayukansu ya kuma mayar da alheri ga mutanen da suka yi asarar dukiyoyinsu.
Dauda Kahutu Rarara
Mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara na daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawar addu’a da kuma aljihunsu,Rarara ya jajantawa al’ummar jahar Borno da kuma mutanen Maiduguri da abin ya shafa,haka zalika ya bayar da gudunmawar abinci da sauran kayan amfani ga wani rukuni na masu gudun hijira a Maiduguri.