• English
  • Business News
Thursday, July 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jaruman Kannywood Da Suka Fi Yawan Mabiya A Shafukan Sada Zumunta

by Rabilu Sanusi Bena
11 months ago
in Nishadi
0
Jaruman Kannywood Da Suka Fi Yawan Mabiya A Shafukan Sada Zumunta
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mafi yawan jarumai a masana’antar Kannywood na amfani da kafafen sada zumunta musamman shafukan Facebook, Tik Tok da kuma Instagram inda sukan dora hotuna, bidiyo da sauran tallace tallace da a kan ba su lokaci bayan lokaci.

Ta wannan hanyar masoyansu da dama kan bibiye su a shafukan domin sake kulla dankon soyayya a tsakaninsu, galibi jarumai mata da maza sukan yi amfani da shafukan sada zumunta domin su kara yawan masoyansu ta hanyar kyawawan hotuna da faya fayen bidiyo don duk su burge mabiya da masoyansu.

  • Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
  • Fina-finai Masu Dogon Zango Koma Baya Ne Ga Masana’antar Kannywood – Tanimu Akawu

A wannan makon Leadership Hausa ta bibiyi shafukann wadannan sanannun jarumai a masana’antar ta Kannywood domin zakulo maku wadanda suka fi saura yawan mabiya a wannan saha ta sada zumunta musamman Facebook, Tik Tok da Instagram.

(10). Abdullahi Amdaz

Kannywood

Labarai Masu Nasaba

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

 

Mabiya Miliyan 2

Wannan jarumin ba boyayye bane a masana’antar Kannywood domin kuwa bayan zamansa jarumi ya na kuma taba wakoki,ya yi shura a shekarun 2022 a lokacin ya fito a cikin shirin fim mai dogon zango na Labarina, rawar da ya taka a wannan shiri ya sa ya tara dimbin masoya a ciki da wajen Nijeriya hakan ya janyo mashi mabiya Miliyan 2 a dukkan kafafen sada zumunta da yake amfani dasu.

(9). Dauda Kahutu Rarara

Kannywood

Mabiya Miliyan 2.4

Mawakin siyasa wanda kuma a wani lokaci yake taba wakokin soyayya a cikin fina finai Dauda Kahutu Rarara, ya tara dimbin masoya sakamakon wakokinsa na siyasa da fina finai, da yake ita siyasa mugun wasa ce inji bahaushe zaman Rarara mawakin siyasa ya sa ya tara masoya kuma a lokaci guda makiya amma duk da hakan bai hana ya samu mabiya Miliyan 2,400,000 ba a shafukansa na Tik Tok, Facebook da kuma Instagram ba.

(8).  Maryam Booth (Dijangala)

Kannywood
Screenshot

Mabiya Miliyan 2.7

Maryam Booth ko kuma Dijangala kamar yadda wasu suke kiranta ta samu daukaka tun bayan fitowarta a cikin wani shiri mai suna Dijangala tare da jarumi Adam A Zango, tun lokacin tauraruwarta ta ci gaba da haskawa duba da cewa kyakkyawar matashiyar ta na taka rawar gani a duk bangaren da aka saka ta a cikin shirin fim, Dijangala ta samu mabiya Miliyan 2,700,000 a shafukan sada zumunta uku da take amfani dasu.

(7).  Nafisa Abdullahi

Kannywood

Mabiya Miliyan 2.8

Nafisa Abdullahi jaruma ce da ta amsa sunanta a masana’antar Kannywood, ta fito a manya manyan fina finai da suka samu daukaka a Duniyar fina finan Hausa, ta haka ne jarumar ta yi suna kuma ta samu dimbin masoya, daga cikin manya manyan fina-finan da jarumar ta fito akwai Marainiya,’Ya Daga Allah, Labarina da sauransu bayan shura a fagen shirye shiryen fim jarumar kuma tayi amfani da wannan dama wajen tara mabiya a shafukan sada zumunta inda ta ke da mabiya fiye da 2,800,000 a shafukanta na Instagram da Tik Tok.

(6). Aisha Humaira

Kannywood

Mabiya Miliyan 4.1

Aisha Humaira ta shahara musamman a manhajar Tik Tok da Instagram inda ta ke dora gajerun bidiyoyi masu kayatar da mabiyanta, Aisha wadda ta ke da kusanci da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a lokuta da dama a kan ganeta ta na dora gajerun bidiyoyin wakokin siyasa musamman wadanda Rarara ya rera da kanshi, a fagen fina finai jarumar ta zama mai daukar nauyin fina finai (furodusa) inda ta shirya fim dinta na farko mai suna  A Cikin Biyu jarumar tanada mabiya Miliyan 4,100,000 a shafukanta na Tik Tok da Instagram.

(5). Adam A Zango

Kannywood

Mabiya Miliyan 4.1

Daya daga cikin jarumai maza da suka dade ana damawa dasu a wannan masana’antar ta Kannywood Adam A Zango, jarumi kuma mawaki ya shafe shekaru fiye da 10 ana ganinsa a cikin manyan fina-finai, ba iya waka da fim kawai Adamu ya tsaya ba hakazalika ya na taba harkar kasuwanci a gefe a kafar sada zumunta kuwa Adamu ya tara mabiya da suka haura 4,100,000 a shafukan sa na Tik Tok,Facebook da shafin Instagram.

(4).  Naziru Ahmed (Sarkin Waka)

Kannywood

Mabiya Miliyan 4.3

Mawakin sarakuna da wakokin soyayya Naziru M Ahmed wanda ake kira da Sarkin Waka ya yi shura a kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da Tik Tok, lokuta da dama mawakin ya kan janyo cece kuce a wadansu rubuce rubucensa kokuma abubuwan da yake dorawa a shafukanshi,kwanakin baya mawakin a wata hira da yayi ya kira matasa masu yin harkar mining na kirifto da suna cima zaune wanda ya matukar bata rayuwar da dama daga cikinsu inda suka dinga kiranye akan mahukuntan Facebook su rufe shafin sarkin wakar, hakan bai hana shi tara mabiya 4,300,000  a dukkan shafukansa uku ba.

(3)   Rahama Sadau

Kannywood

Mabiya Miliyan 4.9

Rahama Sadau ba sabon suna bane a kunnuwan masu sha’awar kallon fina finai hakazalika ba sabuwar fuska ba ce ga masu sha’awar kallon fina finan Hausa da ma na kudancin Nijeriya,Sadau ta zama kallabi a tsakanin rawuna tun lokacin da ta fara wannan harka ta shirin fim,ba a arewacin Nijeriya kadai ba har da kudancin kasar da ma kasashen waje duka sun san wacece Sadau,da  haka ne ta yi amfani da damarta ta hanyar samar wa kanta mabiya Miliyan 4,900,000 a shafukan Facebook, Tik Tok da Instagram.

(2).  Hadiza Gabon

Kannywood

 

Mabiya Miliyan  5.8

Shahararriyar jaruma a masana’antar Kannywood Hadizatu Aliyu kokuma Hadiza Gabon kamar yadda akafi saninta,ta na daya daga cikin manya manyan jarumai da suka ribaci daukakar da Allah ya basu ta hanyar samar wa kansu dimbin masoya a ciki da wajen Nijeriya,Gabon wadda ta shafe shekaru 10 ana damawa da ita a wannan masana’antar ta tara dimbin mabiya a shafukan sada zumunta musamman shafukan Facebook, Tik Tok da Instagram har ta zamo ta daya ga yawan mabiya a shafukan sada zumunta a cikin mata a masana’antar Kannywood ta biyu kuma ga baki daya inda ta ke da mabiya 5,800,000.

(1). Ali Nuhu

Kannywood

Mabiya Miliyan 7.8

Ba abin mamaki bane Sarki Ali Nuhu ya kasance wanda yafi yawan mabiya a shafukan sada zumunta a cikin jaruman masana’antar ta Kannywood,shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya Ali Nuhu Muhammad ya dade ya na jan ragamar wannan masana’antar ta fannin daukaka da sanayya a tsakanin tsararrakinsa jarumai,Sarki kamar yadda ake mashi lakabi ya kasance mutum na farko a duk masana’antar Kannywood da yake da yawan mabiya inda yake da yawan mabiya 7,800,000 a dukkan shafukanshi na sada zumunta da suka hada da Facebook, Tik Tok da Instagram.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Adam ZangoAli NuhuAmdazHadiza GabonJarumar Fina-finan KannywoodKannywoo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Dubban Jama’a A Isra’ila Sun Yi Zanga-Zangar Neman Amincewa Da Yarjejeniyar Hamas

Next Post

Da ÆŠumi-É—umi: Tankar Mai Ta Fashe Ta Kashe Mutane 30 A Neja

Related

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
Nishadi

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

5 days ago
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa
Nishadi

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

3 weeks ago
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau
Nishadi

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

4 weeks ago
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

4 weeks ago
Babu Irin ArziÆ™in Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
Nishadi

Babu Irin ArziÆ™in Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

1 month ago
Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
Nishadi

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

1 month ago
Next Post
Da ÆŠumi-É—umi: Tankar Mai Ta Fashe Ta Kashe Mutane 30 A Neja

Da ÆŠumi-É—umi: Tankar Mai Ta Fashe Ta Kashe Mutane 30 A Neja

LABARAI MASU NASABA

Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

July 31, 2025
NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira

Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC

July 31, 2025
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

July 31, 2025
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

July 31, 2025
Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

July 31, 2025
Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

July 31, 2025
Gwamnatin Borno Ta Nada Kwamitin Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi

Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu

July 31, 2025
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

July 31, 2025
Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

July 31, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira

Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira

July 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.